Kasashe 15 na duniya ne za su shiga gasar karatun Al-Qur'ani da ke tafe, ciki hada Nijeriya

A wani yunkurin inganta hadin kai da bunkasa ilimi, fiye da makarata ALQUR'ANI MAI GIRMA 80 daga fadin duniya ne suka gudanar da taro a gidan tsohon Dan Majalissar Wakilai ta tarayya Mai wakiltar mazabar Bassa da Jos ta Arewa Honourable Muhammad Adam Alkali OON. (Garkuwan Gwanayen AlQur'ani na kasa)

Taron nada nufin shiryawa gasar karatun ALQUR'ANI MAI GIRMA ta Kasa da Kasa dake tafe Wanda Majlis Ahlul Qur'an ta shirya, kar kashin jagoranci Hon. Gwani Muhammad Adam Alkali OON .

Gasar wadda za a sanar da ranar da zata gudana nan bada dadewa ba nada nufin habbaka karatu da haddar ALQUR'ANI MAI GIRMA tare da inganta hadin kai a tsakanin mahalarta gasar.

Makaranta ALQUR'ANI MAI GIRMA daga kasashe 15 ne zasu fafata a bangarori da daban daban domin baje baiwar da Allah ya hore masu a fannin karanta Littafi Mai Tsarki.

Gasar karatun ALQUR'ANIN zata kunshi ingattun Alkalai da Masana wadanda zasu tantance kwazo da kwarewar mahalarta gasar.

Gasar kuma zata bada dama ga makaranta ALQUR'ANI MAI GIRMA su nuna basirar su tare da kara koyon yadda ake karanta ALQUR'ANIN.

Kungiyar data shirya gasar Mai suna Majlis Ahlul Qur'an, kungiya ce dake a Najeriya wadda ta kudiri aniyar habbaka zaman lafiya da hadin kai ta hanyar karatu da nazarin ALQUR'ANI MAI GIRMA.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp