Karin kudin man fetur zai munana irin talaucin da ma'aikatan Nijeriya ke ciki-kungiyar TUC

Karin kudin man fetur zai munana irin talaucin da ma'aikatan Nijeriya ke ciki-kungiyar TUC

Hadaddiyar kungiyar kwadago ta Nijeriya (TUC) ta yi fatali da karin farashin man fetur na baya-bayan nan, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kara ta’azzara talauci a tsakanin ma’aikata.


Kungiyar ta bayyana matsayin ta ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.


Shugaban kungiyar ta TUC, Kwamared Festus Osifo, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar soke wadannan shawarwari, ta inganta manufofin da za su karfafa Naira, da kuma daukar kwararan matakai don rage radadin da ’yan Nijeriya ke ciki.


Ta yi nuni da cewa ba zato ba tsammani an kara farashin ba tare da tuntubar al'umma ba, yana nuna rashin kula da jin dadin al’ummar Nijeriya, musamman ma’aikatan da ke da alhakin irin wadannan shawarwari.


Ya kara da cewa yunkurin  kara farashin mai da wutar lantarki ba zato ba tsammani zai kara ta'azzara wahalhalun da ake ciki ga al'umma.


Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta soke wadannan abubuwa, ta inganta manufofin da za su karfafa Naira da kuma daukar kwararan matakai don rage radadin ’yan Nijeriya. Dole ne gwamnati ta yi gaggawar maido da kwarin gwiwa tare da hana ci gaba da tabarbarewar yanayin rayuwar 'yan kasarta.


Domin TUC ta damu matuka da karin farashin wutar lantarki da kashi 250 cikin 100, inda ta ce wutar lantarki na da matukar muhimmanci ga rayuwar marasa galihu a cikin al’umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post