Karin kudin man fetur: Gwamnatin Edo ta dage komawa makaranta

Karin kudin man fetur: Gwamnatin Edo ta dage komawa makaranta 

Gwamnatin jihar Edo ta dage komawa makaranta saboda tashin farashin man fetur da kalubalen da iyaye ke fuskanta.


A ranar litinin 9 ga watan Satumba ne za a koma makarantu a galibin sassan Nijeriya.


A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta sanya wa hannu, tace an dage ci gaba da aiki a duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu,har sai an sanar da su zuwa.


Sanarwar ta kara da cewa wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ta bayar da umarnin cewa makarantu za su cigaba da kasancewa a rufe saboda tashin farashin man fetur da kuma kalubalen da iyaye da masu kula da yara ke fuskanta.


A baya-bayan nan ne kamfanin mai na (NNPCL) ya kara farashin man fetur zuwa ₦ 855 karin kudin da kamfanin man fetur na kasar ya yi ya sanya wasu 'yan kasuwa sayar da man sama da ₦900 kan kowace lita, inda wasu ke sayar da shi sama da ₦1000 kan kowace lita.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp