Jam'iyyar Labour ta musanta cewa dan takarar ta na gwamna a Edo ya janye daga takara

 Jam'iyyar Labour ta musanta cewa dan takarar ta na gwamna a Edo ya janye daga takara

Jam’iyyar Labour reshen jihar Edo ta musanta rahotannin da ke cewa dan takararta na gwamna Barista Olumide Akpata ya ajiye takara ya marawa dan jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo, baya a zaben ranar Asabar.


Wata wasika da ake zargin Akpata ne ya rubuta kuma ya sanya hannu a halin yanzu tana ta yawo a shafukan sada zumunta.


A cikin wasikar tana cewa, Akpata ya janye wa dan takarar jam’iyyar PDP a zaben bayan tuntubar juna sosai.


Sai dai, sakataren yada labaran jam'iyyar Labour Sam Uroupa, ya karyata rahoton, yana mai cewa har yanzu yana cikin takara kuma zai lashe zaben.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp