Jami’an ‘yan sanda 32 ne kawai ke tsare kauyuka 200 a Katsina – Gwamna Radda

Jami’an ‘yan sanda 32 ne kawai ke tsare kauyuka 200 a Katsina – Gwamna Radda

Gwamnan jihar Katsina Dikko Ummar Radda ya sake yin tsokaci kan kalubalen tsaro da ke ci gaba da addabar jihar.


Yayin da yake hira da DW Hausa, gwamnan ya ce jami’an ‘yan sanda 32 ne kawai ke sintiri a karamar hukuma daya a jihar.


Gwamnan, wanda bai bayyana ko wane daga cikin kananan hukumomin ba, ya ce ya kunshi unguwanni 10 da kauyuka sama da 200.


A cewarsa, a cikin jami’an 32, bindigu guda tara ne kawai ke da su, inda guda biyar kacal suke aiki.


Ya ce a yanzu haka a Katsina akwai karamar hukuma mai ‘yan sanda 39 da bindigu guda tara, kuma bindigogin da zasu iya aiki su biyar ne.


Mun bullo da wani shiri wanda duk wata al’umma da ke shirye ta kare kanta, za mu ba su goyon baya da horon da ya dace don kare kai kafin zuwan jami’an tsaro.


Katsina ta sha fama da munanan hare-hare daga ‘yan bindiga.


Ko a kwanakin baya Gwamna Radda ya yi kira ga al’ummar jihar da su dauki matakan kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.


Ya yi wannan jawabi ne a wani taro da aka yi a Daura.


A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, Radda ya fusata sosai, ya kuma bukaci malaman addinin Musulunci da su fadakar da 'yan kasar muhimmancin kare kai kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp