Jami’an tsaro sun kama alburusai 610 a Katsina
Jami’an tsaron da gwamnatin jihar Katsina ta kafa,na Community Watch Corps, sun cafke wata mota makare da alburusai 610 a karamar hukumar Batsari da ke jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Nasir Muazu ya fitar ranar Laraba a Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Batsari na daga cikin kananan hukumomin da ke kan gaba wajen fuskantar matsalar rashin tsaro.
Yace jami’an mu sun gudanar da wani gagarumin aiki a ranar 10 ga Satumba, 2024, da misalin karfe 7:30 na dare, a garin Batsari.
A bisa ga sahihan bayanan sirri, jami'an sun kama wata motar haya, dauke da fasinjoji 17 – mata 13 da maza hudu, ciki har da direban motar.
A lokacin da jami’an suke gudanar da bincike a wani shingen binciken ababen hawa, sun gano tarin alburusai da aka boye a karkashin kujerar mota, inda daga baya aka gano akwai harsashin harsasai 610 na AK-47 da kuma Mashin.