Shugaba Bola Tinubu ya amince da Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa shekarar 2027.
Dangane da rahotannin da ke cewa an tsawaita wa’adin aikinsa, wata majiya mai tushe daga ‘yan sanda, da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa wasikar ba ta tsawaita wa'adin nasa ba, ta dai tabbatar da ya kammala wa’adin sa na shekaru hudu kamar yadda ya bayyana a wasikar nadin nasa.
Majiyar ta ce, ba a tsawaita wa’adin IGP din ba, sai dai an yi karin haske kan wasikar nadin nasa wadda ta kunshi shekaru hudu a matsayin shi na babban sufeton 'yan sandan Nijeriya.
A watan Yuli ne dai majalisar dokokin kasar ta zartar da dokar gyaran dokar ‘yan sanda domin baiwa mutumin da aka nada a ofishin babban sufeton ‘yan sandan kasar damar ci gaba da rike mukaminsa har zuwa karshen wa’adin da aka tanadar a cikin takardar nadi.
Shugaba Tinubu ya mika kudirin dokar ga majalisar wakilai da ta dattawa domin yin kwaskwarima ga dokar.
‘Yan majalisar sun yi gaggawar zartar da kudurin dokar a zauren majasun duka.
Shugaban ya nada Egbetokun a matsayin IGP a watan Yunin 2023 na tsawon shekaru hudu. An nada shi tare da sabbin shugabannin hukumomin tsaro guda hudu.
Dangane da sashe na 18 (8) na dokar ‘yan sanda ta 2020, Egbetokun, wanda aka haifa a ranar 4 ga Satumba, 1964, ana sa ran zai yi ritaya a watan Satumba na 2024, lokacin da ya cika shekaru 60.
A halin yanzu dai Egbetokun ya shafe shekara daya da wata uku a kan karagar mulki, saura shekaru biyu da wata tara a ya cike shekaru hudu a nadin nasa.