Hukumar kwastam ta fara bincike kan zargin karbar kudaden da wasu jami'anta ke yi a hannun wasu 'yan kasuwa a Kano

Hukumar kwastam ta fara bincike kan zargin karbar kudaden da wasu jami'anta ke yi a hannun wasu 'yan kasuwa a Kano

Hukumar Kwastam ta Nijeriya reshen Kano-Jigawa ta kaddamar da fara bincike kan zargin karbar wasu kudade da jami’anta ke yi ‘yan kasuwa a kasuwar Abubakar Rimi da aka fi sani da Sabon Gari a Kano.


‘Yan kasuwar sun koka kan yadda wasu jami’an hukumar kwastam ke karbar makudan kudade, miliyoyin nairori daga wajensu.


Nazifi Auwalu,shine jami’in hulda da jama’a na kungiyar 'yan kasuwa da ‘yan kasuwar ta yanar gizo, ya bayyana yadda hakan ke jawo wa ‘yan kasuwar matsala.


Yace yanzu suna cikin wani mawuyacin hali na kawo kayayyaki cikin jihar Kano,jami’an hukumar kwastam suna bin 'yan kasuwa a ko’ina, suna kame kayayyakin su a cikin jihar, duk da cewa babu wata iyaka a Kanon, yawancin kayayyakin da suke sayarwa ana samo su ne a cikin gida Nijeriya, musamman daga Legas.


Ya ba da misali da wani lamari na baya-bayan nan inda jami’an hukumar kwastam suka kama wata mota dauke da turare da suka zarge su da safarar haramtattun kayayyaki. Duk da binciken da aka yi na gano cewa babu wani haramtaccen kaya, jami’an sun bukaci naira miliyan daya domin sakin motar.



A martanin da jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam ta Kano-Jigawa Nura Abdullahi ya mayar ya tabbatar da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin kamar yadda ya bayyanawa Daily Trust.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp