Hukumar ICPC na tuhumar Chris Ngige minista lokacin mulkin Shugaba Buhari kan batun wasu kwangiloli
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta gayyaci Chris Ngige, daya daga cikin ministocin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari domin amsa tambayoyi.
Ngige, wanda ke kula da ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, an yi masa tambayoyi kan rawar da ya taka a wasu kwangiloli da ayyukan yi da suka faru a daya daga cikin hukumomin a lokacin da ya rike madafun iko.
An bayyana cewa tsohon Ministan ya kasance tare da jami’an hukumar ICPC na tsawon sa’o’i biyar a ranar Laraba domin amsa wasu tambayoyi kan yadda aka bayar da wasu kwangiloli a asusun inshorar jama’a na Nijeriya NSITF.
A baya dai Daily Trust ta bayyana yadda ICPC ta gayyaci wasu manyan jami’an NSITF domin amsa tambayoyi kan biyan N47m gratuity ga tsohon shugaban hukumar, Mrs Maureen Allagoa, a lokacin da take aiki.
Hakazalika, tsohon Ministan Kwadago, Simon Lalong, wanda yanzu haka yake a Majalisar Dattawa, ya kafa kwamitin bincike na musamman don binciki badakalar bada kwangilar da aka bayar na N1.8bn a hukumar.
Tuni dai hukumomin yaki da cin hanci da rashawa — ICPC da EFCC suka shiga cikin lamarin tare da gayyata ta baya-bayan nan ga tsohuwar ministar. An gayyaci Ngige ne a lokacin da yake kasar Amurka domin duba lafiyarsa.