Haryanzu kamfanin NNPCL Ltd bai fara daukar man fetur din mu ba - Dangote

Haryanzu kamfanin NNPCL Ltd bai fara daukar man fetur din mu ba - Dangote

Kamfanin Dangote ya yi watsi da rahotannin da ke cewa kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya fara daukan man fetur daga matatarsa.


Wata jarida ta ruwaito cewa NNPCL ya dauko man fetur daga matatar Dangote ya sayar wa ‘yan Nijeriya kan Naira 897 kan kowace lita.


Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote ya bayyana cewa matatar ta shirya don fara hakowa da sayar da man fetur.


Sai dai kuma, Anthony Chiejina, Babban Daraktan Sadarwa na Rukunin Dangote, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce har yanzu kamfanin na NNPC bai fara dauke mai daga matatar man ba.


A cewar Rukunin Dangote, kasuwar man fetur tana da ka’ida sosai, don haka kamfanin ba zai iya tantancewa,ko tasiri kan farashin man da ke karkashin kulawar hukumomin gwamnati da abin ya shafa ba.


Muna so mu bayyana cewa NNPC bai fara daukar tataccen mai ba.


Don haka batun kayyade farashin man fetur da aka ce anyi daga matatar man bai taso ba, domin har yanzu ba mu kammala kwantiragin mu da NNPC ba.


Kasuwar PMS tana da kayyadadden tsari, wanda duk ‘yan kasuwar mai da masu ruwa da tsaki a fannin suka sani, don haka ba za mu iya tantancewa ba.


Muna kira ga jama'a da su yi watsi da labaran da ake yadawa domin yaudara ce kuma ba gaskiya a wannan lamari. Muna ba wa ‘yan Nijeriya tabbacin samun ingantataccen man fetur da za a samu cikin sauki a duk fadin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post