Gwamnatin Zimbabwe ta amince da yanka giwaye 200 don ciyar da 'yan kasar da ke fama da yunwa

Gwamnatin Zimbabwe ta amince da yanka giwaye 200 don ciyar da 'yan kasar da ke fama da yunwa

Mai magana da yawun hukumar kula da wuraren shakatawa da namun daji na Zimbabwe, Tinashe Farawo, ya tabbatar wa CNN da haka a ranar Litinin.


Farawo, yace sakamakon tsananin fari a kasar da ake fama dashi a gabashin Afirka yasa aka yanke wannan hukunci domin a baiwa al'ummar kasar.


Ya kara da cewa dabbobin suna yin barna sosai a cikin al’umma, suna kashe mutane,ko a makon da ya gabata an rasa wata mata a yankin arewacin kasar da giwa ta kashe. 


A cewar kafafen yada labarai na cikin gida, a bana, sama da mutane 30 ne namun daji suka kashe da na a lokuta daban-daban a Zimbabwe.


Kamfanin dillancin labaran reuters ya rawaito Farawo ya ce wannan matakin na kuma daga cikin kokarin da kasar ke yi na rage cunkoso a wuraren shakatawa na kasar, wadanda ke iya daukar giwaye 55,000 kawai.Zuwa yanzu dai kasar Zimbabwe tana da giwaye sama da 84,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp