Gwamnatin jihar jigawa ta bayar da jari ga mata sama da dubu 12,a jihar

Gwamnatin jihar jigawa ta bayar da jari ga mata sama da dubu 12,a jihar

Gwamnan jihar jigawa Mallam Umar Namadi ya kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin mata na JCARES a fadin jihar a yankin Gwari da ke karamar hukumar Dutse.


A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Namadi ya bayyana mahimmancin sabon shirin na karfafa tattalin arzikin mata, wanda ya shafi mata sama da 12,600 a fadin jihar inda kowanen su za ta samu tallafin kudi naira 50,000, jimilla ₦630 miliyan na tallafin tattalin arziki.


Gwamna Namadi ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tabbatar da cigaban al'umma,wanda ya ba da fifiko wajen karfafawa matasa da mata da hanyoyi da rayuwarsu za ta inganta.

Ya kuma jaddada muhimmancin mayar da hankali ga mata wadanda ke da kashi 51% na al’ummar Jihar Jigawa, don tabbatar da bunkasar tattalin arzikinsu da inganta rayuwar iyalansu da al’ummarsu.


Gwamnan ya kuma sanar da kaddamar da wani sabon shiri na tallafawa mata tare da hadin gwiwar bankin duniya mai suna Nigeria for Women Project. Wannan shiri dai zai shafi dubban mata ne, tare da samar musu da abubuwa masu amfani da kuma shawo kan matsalolin cibiyoyi da kasuwanni domin bunkasar tattalin arzikin su.


Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin kudi na N50,000 da su yi amfani da kudaden domin bunkasa tattalin arzikin su domin samun ingantacciyar rayuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post