Gwamnatin Jigawa za ta kashe N300bn a fannin lafiya,Ilimi da samar da hanyoyi

Gwamnatin Jigawa za ta kashe N300bn a fannin lafiya,Ilimi da samar da hanyoyi 

Gwamnatin jihar Jigawa za ta kashe sama da Naira biliyan 300, da nufin inganta hanyoyin da jihar ke da su, da ilimi da kuma fannin kiwon lafiya.


A zaman da majalisar zartaswar jihar ta yi a jiya, Gwamna Malam Umar Namadi ya jaddada aniyar gwamnati na samar da ababen more rayuwa ga al'ummar Jihar.


Gwamna Umar Namadi ya ce wadannan ayyuka za a yi su ne domin bunkasa tattalin arziki, da inganta rayuwa, da kuma sanya jihar Jigawa a matsayin cibiyar zuba jari da ci gaba.


Gwamnan ya bayyana cewa an bayar da kwangilar ginawa da gyaran hanyoyi guda 45, wanda ya kai kilomita 835.36, duk cin Naira biliyan 300.46.


Sauran ayyukan sun hada da biliyan 16.03 na kiwon lafiya, sai miliyan 473.62 na samar da ruwa, da kuma miliyan 871.69 na ilimi.


Don tabbatar da kammala aikin a kan lokaci, ya ce gwamnati ta amince da biyan kashi 10% na jimillar kudaden kwangilar da aka baiwa ayyukan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp