Gwamnan Sokoto ya gargadi ‘yan siyasa da su daina siyasantar da matsalar tsaro

Gwamnan Sokoto ya gargadi ‘yan siyasa da su daina siyasantar da matsalar tsaro

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya gargadi mutane ko kungiyoyi da su daina siyasantar da matsalar tsaro a jihar.


Ya yi wannan gargadin ne a wata ziyarar godiya da ya kai karamar hukumar Goronyo a ranar Asabar.


Yace tsaro wani lamari ne mai mahimmanci wanda ya shafi kowa da kowa, kuma ba za su lamunci da duk wani yunƙuri na amfani da shi don cin riba ta siyasa ba.


"Saboda haka, ina kira ga kowa da kowa da ya guji yin kalamai masu tayar da hankali ko kuma daukar matakan da za su kawo cikas ga lafiyar ‘yan kasar,”


Gwamnan, ya jaddada cewa tsaro wani nauyi ne da ya rataya a wuyansa, don haka ya bukaci hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki.


Gwamnan ya kara da cewa, "Ba za mu amince da duk wani mai kokarin sanya siyasa a harkokin tsaro ba, kuma za mu dauki matakan da suka dace don hana irin wadannan ayyuka kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu.

1 Comments

  1. Your Excellency, That is the nature of todays society. We're in Democratic Era, You've to bear all the critism that will transfers in your airs. If you can't tackle the problem of Insecurity in your State, So,
    You better resign.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post