Gobara ta tashi a gidan gwamnatin jihar Katsina

 


Gobara ta tashi da sanyin safiyar Litinin, ta kone wani sashe na babban dakin taro na gidan gwamnan jihar Katsina.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban dikin taron (red chamber)na  kusa da ofishin gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda inda ya ke ganawa da muhimman mutane.

Ya zuwa hada wannan rahoto babu wani takamaiman musabbabin tashin gobarar da barnar da ta yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post