Ganduje ya musanta shirin tsige Sarki Sanusi
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje, ya ce babu gaskiya cikin zargin da ake yi masa na alakanta shi da wani sabon yunkurin tsige Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.
Hakan na zuwa ne biyo bayan wani rahoto da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta mai taken, Ganduje ya jagoranci wani sabon shiri na tsige Sarki Mohammad Sanusi.
A lokacin baya an tsige tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya a zamanin gwamnatin Ganduje yana gwamnan jihar.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis, Ganduje, wanda ya yi magana ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan wayar da kan jama’a, ya barranta kan sa daga yunkurin tsige Sarkin Kano na 16 kuma shugaban majalisar sarakunan jihar.