Farashin tsohuwar masara ya tashi a wasu kasuwannin Nijeriya


A yayinda sabbin kayan amfanin gona ke fara shigowa kasuwannin jihohin Nijeriya, wasu tsoffin kayan abincin kuwa na kara tsada a wasu kasuwannin kasar.

A wannan mako ana sayar da buhun tsohuwar masara N90,000 a jihohin Adamawa da Legas, to a makon jiya ma haka aka sai da a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas.

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina N93000 aka sai da a makon daya gabata, yayinda a wannan mako aka sayar da ita N92000

A kasuwar Dandume jihar Katsina N85,000-88000 ake sayar da buhun masarar a wannan satin, amma a makon daya gabata N88000-90,000 aka sayar da buhun.

Sai kasuwar Giwa jihar Kaduna ana sayar da buhun N83000 a wannan sati.

Masarar tafi sauki a kasuwar Dawanau a jihar Kano da ake sayar da ita akan N80,000 daidai a makon nan da ke shirin karewa, bayan da a makon jiya aka sayar da ita N90,000.

Ita kuwa Shinkafar Hausa tashi ta yi a kasuwannin jihar Adamawa wanda ake sayar da buhunta N180,000 a wannaan satin, amma a makon daya shude N156-160,000 aka sayar da buhun a kasuwar.


A kasuwar Dawanau jihar Kano an sayi buhun Shinkafar N160,000 a satin da wuce, amma a makon nan N155,000 ne kuɗinta.


A 'yan kwanakin nan dai shinkafar Hausa tafi sauki a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a kudancin Nijeriya, inda ake sayar da ita akan N135,000 a wannan satin, yayinda a makon daya gabata aka sayar da ita a N140,000 daidai.


N145,000 ake sayar da buhun shinkafa 'Yar gida a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da kasuwar Giwa jihar Kaduna a wannan mako.


An sayi buhunta N165-170,000 a kasuwar Dandume jihar Katsina a makon daya gabata, yayin da a wannnan mako ake sayar da buhun sabuwar Shinkafar kan kuɗi N120,00-1220000.


To a bangaren Shinkafar waje ma tafi sauki a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ake sayar da ita a N70,000 cif a makon nan da ke mana bankwana, bayan da a makon jiya aka sayar da ita N73000.


Farashin Shinkafar Bature bata sauya zani ba dana makon jiya da ake sayar da ita N80,000 daidai a kasuwannin jihar Adamawa, haka nan ake sayar da ita a makon nan.


Ana sayar da Shinkafar waje a kasuwar Dawanau jihar Kano N97000 a wannan farko na watan na Satumban 2024, amma a makon daya shude N95000 ne kuɗinta.


To a kasuwar Giwa jihar Kaduna N85000 ne ake sayar da buhun shinkafar a wannan satin.


N83000 ake sayar da Buhunta a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a makon nan mai karewa, haka kuma aka sayar da ita a makon jiya.


A Kasuwar Dandume jihar Katsinan N72000 kuɗin buhun Shinkafa 'yar Gwamnati a wannan mako, amma a makon daya gabata N75000 aka sai da buhun.


Farashin tsohon wake ma dai bai sauya zani ba dana makon jiya wanda aka saida N190000-200,000 a kasuwannin jihar Adamawa, to sai dai N170,000 ne ake sayar da buhun sabon wake a kasuwar a wannan satin nan.


A kasuwar Giwa jihar Kaduna ana sayar da buhun farin wake N180,000 daidai a wannan mako.


Tsohon wake yafi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas da ake saidawa N240,000 a makon nan, bayan da a makon jiya aka sayar N180,000.


A kasuwar Dandume jihar Katsina ana sayar da buhun N140,000-150,000 a wannan mako, yayinda a makon daya gabata aka sai da N185,000


Farashin wake bai canza zani ba dana makon jiya, wanda aka sayar N135,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano, haka nan ake sayar wa a wannan satin nan.


N120,000 ake sayar da buhun kananan wake a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan mako.


To bari mu kammala farashin kayan abinci na makon nan da Spaghetti.


Inda Har yanzu farashin taliyar yaki sauka a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ke jihar Legas wanda ake saidawa N19000. 


A jihar Adamawa ma dai farashin bai sauya ba dana makon daya gabata da aka sayar da ita N17600.


N19,500 ake sai da kwalin taliyar a kasuwar Dawanau jihar Kano a makon nan, bayan da a makon jiya aka sayar N19,000 cif.


An samu karin N500 kan farashin taliya da aka sayar N19,500 a kasuwar Dandume jihar Katsina a makon jiya, amma a makon nan N20,000 ake sayar da ita.

A Mai'adua jihar Katsina N17,400 aka sayar da kwalin taliya a makon daya gabata, amma a makon nan N17000 ake sayar da Kwalinta.

DCL Hausa A'isha Usman Gebi

Post a Comment

Previous Post Next Post