Farashin litar fetur ya kai N1,200 a Kano


Farashin litar man fetur ya daga zuwa sama, inda ya koma N1,200 a wasu gidajen mai a Kano, yayin da wasu gidajen mai mallakin kamfanin NNPC farashin ya koma N904.

Jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa yanzu haka layukan man fetur sun yi tsawo musamman a gidajen mai na NNPC biyo bayan samun labarin tashin farashin litar man.

Wani jami'i a wani gidan man NNPCL da ya nemi jaridar ta sakaya sunansa ya ce suna jiran umurni ne daga sama kafin su fara sayar da man a sabon farashi.

Sai dai wata takarda da DCL Hausa ba ta tabbatar da sahihancinta ba daga kamfanin NNPC ta ce har yanzu ba kamfanin bai ba da sabon umurnin sayar da fetur din a wannan sabon farashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post