Farashin tsohon masara bai sauya zani ba a kasuwannin jihohin Adamawa da Legas da aka sai da N90,000 daidai a makon daya gabata,haka nan ake saidawa a makon nan.
A kasuwar Giwa jihar Kaduna N82,000 ake sayar da buhun masara a wannan sati, amma a makon jiya N83,000 aka sai da buhun, an samu sauƙin N1000 kenan a mako guda.
Har yanzu Shinkafa 'yar gida tafi tsada a kasuwannin jihar Adamawa da ake saidawa N168,000 a satin nan da ke dab da ƙarewa, yayinda a makon daya wuce aka sayar kan kuɗi N180,000.
An samu ragin N5000 kan farashin shinkafar Hausa a kasuwar Dawanau jihar Kano da aka sai da N155,000 a makon daya gabata,amma a wanna mako N150,000 ne ake sayar da buhun.
Ita kuwa kasuwar Mai'adua jihar Katsina karin N5000 aka samu kan farashin makon jiya da aka saya N145,000, yayin da a wannan mako ake sai da buhun shinkafa 'Yar gida N150,000 cif.
Shinkafar Hausa na ci gaba da sauka a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a kudancin Nijeriya, inda ake sayar da ita N130,000 a wannan satin, bayan da a makon daya shude aka sayar da buhun N135,000.
A kasuwar Giwa jihar Kaduna farashin bai sauya dana makon jiya da aka sayar N145,000.
Shinkafar Bature kuwa na ci gaba da jan akalarta a kasuwar Dawanau jihar Kano da ake sayar da ita akan N100,000 cif a wannan makon, amma a makon daya wuce N97,000 ne aka sayar da buhun.
Sai dai shinkafa 'Yar Gwamnatin tafi sauki a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas wacce ake sayar da ita N73,000 a makon nan, yayinda a makon jiya aka sai da ta N70,000 daidai.
To a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa N85-90,000 ake sayar da Buhun a wannan mako, amma a makon jiya N80,000 daidai aka sayar da buhun.
Sai kasuwar Mai'adua jihar Katsina ana sayar da buhun shinkafar waje N81000 a wannan satin, sai dai a makon daya gabata N83000 aka sai da buhun, an samu saukin N2000 kenan a wannan makon da ke mana bankwana.
Sai dai kuma farashin Shinkafar Bature ta kara kudi a kasuwar Giwa jihar Kaduna, inda aka sayar da ita N85000 a makon daya gabata, amma a makon nan N87,000 ake sayar da buhun.
To bari mu leka bangaren farashin wake domin ganin me ke wakana
Sabon waken yafi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas wanda ake sayar da shi akan N180,000 a makon nan, sai dai a makon jiya N240,000 aka sai da buhun tsohon wake a kasuwar.
Sai kasuwannin jihar Adamawa ana sayar da buhun sabon wake N165,000,shi kuma tsohon ake saidawa N180,000 a makon nan,amma a makon daya shude N190,000-200,000 aka sai da buhun tsohon waken.
N145,000 ne ake sayar da Buhun farin wake a kasuwar Dawanau jihar Kano a makon nan,amma a makon daya gabata N135,000 aka sai da buhun.
Farashin kananan wake bai canza ba dana makon daya shude da aka saya N120,000 daidai a kasuwar Mai'adua jihar Katsina,haka nan aka sai da a wannan mako.
An samu karin N10,000 kan farashin buhun wake a kasuwar Giwa jihar Kaduna, wanda a wannan makon aka sayar dashi N190,000, bayan da makon jiya aka saida shi N180,000 cif.
A ɓangaren taliyar Spaghetti tafi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legos inda ake saidata N20,000 a wannan satin, yayinda a makon daya shude aka sayar N19000.
Sai jihar Adamawa da ake sai da Kwalinta N17400 a makon nan, amma a makon jiya N17600 aka sai da kwalin.
To a jihar Kano farashin Kwalin taliyar bata sauya zani ba dana makon jiya wanda aka sayar kan kuɗi N19500.
A kasuwar Mai'adua jihar Katsina N17400 aka sai da taliyar Spaghetti a makon daya wuce,yayinda a wannan mako ake saidawa N19000.
N19500 ake sayar da kwalin taliya a kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon nan da ke shirin karewa.
DCL Hausa A'isha Usman Gebi.