Dole ne a kawo karshen rashin tsaro a yankinmu a yanzu – Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF
Bayan wani babban taro da masu ruwa da tsaki a Arewa da suka hada da tsaffin gwamnonin jihohi, ministoci, shugabannin hukumomi, ‘yan majalisar dokoki ta kasa, manyan jami’an gwamnati da suka yi ritaya, malamai, kwararru da sauran ‘yan kasa masu kishin kasa, kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta yi kira da a dauki matakin gaggawa dan kawo karshen matsalar tsaro a Arewcin Nijeriya.
Farfesa Tukur Muhammad-Baba, shine sakataren yada labarai na ACF na kasa, ya karanta sanarwar bayan taron kwamitin amintattu (BoT). Ya soki dabarun da ake bi a yanzu na yaki da masu tada kayar baya da ‘yan bindiga, yana mai cewa,ya ce akwai bukatar a sake salon yadda ake fada da 'yan bindiga .
Tun da farko, shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Bashir Muhammad Dalhatu, ya bayar da uzuri ga al’ummar Arewacin Nijeriya dangane da gazawar da shugabannin suka yi wajen kare yankin daga daya daga cikin munanan rikice-rikice a cikin tarihin yankin.
Dalhatu ya jaddada cewa, ACF na yin nazari sosai kan dabarun magance matsalolin da ake fuskanta a Arewa da Nijeriya baki daya. Ya kuma bayyana cewa Arewa a shirye ta ke ta goyi bayan sake duba kundin tsarin mulki da kuma sauye-sauyen da aka zo dashi.
An kira taron ne domin magance tabarbarewar tsaro, tsadar rayuwa, fatara, rashin aikin yi, da sauran rikice-rikicen da suka addabi Arewacin Nijeriya.
Ta kuduri aniyar cewa dole ne ‘yan Arewa su himmatu wajen rikon amana da hadin kai a tsakanin su, ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba. An yi kira ga membobin da su guji kalaman batanci ga 'yan uwansu.