Buhun masara yafi tsada a kasuwannin jihohin kudancin Nijeriya


Tsohuwar Masara tafi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a kudancin Nijeriya a makon nan me karewa da ake sayar da ita kan kudi N95000,yayinda a makon jiya aka saya  N90,000 cif,sai dai kuma N85,000 ake sayar da sabuwar  masara a kasuwar.

Tsohuwar masara tafi sauki a kasuwar Dandume jihar Katsina da ake sayar da ita N70,000-75000 a makon nan.

To a kasuwannin jihar Adamawa an sayar da buhun tsohuwar masara N90,000 a makon daya gabata,yayinda a makon nan ake sayarwa N85000-90,000.

An samu sauƙin N6000 kan farashin  buhun tsohuwar  masara  a kasuwar Mai'adua jihar katsina inda  aka sayar da ita N93000 a makon daya shude,amma a makon nan N87,000 ake sayar da buhun masarar.

Farashin buhun masara ya sauƙa a kasuwar Giwa jihar Kaduna inda ake saida ta N75000 a wannan mako,amma a makon jiya N82,000 aka sai da buhun.

Farashin shinkafa yar gwamnati ya Karu da N2000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas, inda ake sayar da ita N75000 a makon nan,yayinda a makon jiya aka sai da ta N73,000 daidai.

To a kasuwar dandume jihar Katsina farashin Buhun shinkafar wajen N75000 ne a makon nan,an kuma sayar  da ita N81000 a makon daya gabata.

Sai kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa  inda ake sayar da Buhun N85000 a wannan mako,amma a makon jiya an sayar da ita N85000-90,000.

 Farashin Shinkafar Bature  a kasuwar Giwa jihar Kaduna na nan dai dai dana wancan makon da aka sayar da ita kan kudi N85000 ko wanne buhu. 

Ina ma'abota cin alala da Kosai,sai in ce ku gyara zama don jin farashin wake na makon nan.

Ana sayar  da sabon wake N180,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas kamar dai na makon daya wuce ,yayinda farashin tsohon wake yakai N270,000 an samu karin N30,000 sabanin a makon daya wuce da aka sayar N240,000.

A kasuwar Dandume jihar katsina ana sayar da waken a kan N160,000- 220,000 a makon nan

Sai kasuwannin jihar Adamawa da farashin sabon waken bai canza  ba dana wancan makon da aka sayar  N165,000 shi ma  tsohon waken an cigaba da saidawa kan

Kudi N180,000 kamar dai  makon daya gabata.

N118,000 ake sayar da kananan  wake a kasuwar Mai’adua jihar katsina a satin nan, inda a makon daya shude aka sayar kan kudi N120,000 dai dai.

An samu karin N20,000 kan farashin buhun wake a kasuwar Giwa jihar Kaduna, wanda a wannan makon ake sayar dashi N210,000 , bayan da a makon jiya aka saida shi N190,000 a kasuwar.

Har yanzu  Shinkafa 'yar gida tafi tsada a kasuwannin jihar Adamawa da ake saidawa kan kudi  N152,000- 168,000 a satin nan da ke dab da ƙarewa, yayinda a makon daya wuce aka sayar 168,000

Ita kuwa kasuwar Dandume a jihar Katsina ana sayar da shinkafar kan kudi N135,000 - 140,000 a makon nan mai ƙarewa.

Haka zalika  kasuwar Mai'adua jihar Katsina farashin shinkafar yar gida bai sauya zani ba inda ake sayar da ita kan kudi N145,000 kamar dai yadda aka sayar a wancan  makon.

Shinkafar Hausa ta kara farashi da naira N5000,a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a kudancin Nijeriya, inda a wannan satin ake sayar da ita N135,000 bayan da a makon daya shude aka sayar da buhun N130,000

A kasuwar Giwa jihar Kaduna farashin shinkafar ta gida ya sauka da N5000 inda ake sayar da ita kan N140,000 a makon nan,  yayinda a makon jiya aka sayar da ita N145,000

A ɓangaren taliyar Spaghetti  kua a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legos farashin ta  na N20,000 na nan kamar dai na makon Jiya.

N20,000 ake sayar da  Taliyar a kasuwar Dandume jihar katsina a makon nan.

Sai  jihar Adamawa da ake sai da Kwalinta N17400 - 18,000 a wannan satin, amma a satın daya gabata N17600 aka sai da Kwalinta.

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina N17400 aka sai da taliyar Spaghetti a makon daya wuce,yayinda a wannan mako ake saidawa N19200.

An samu karin N1800 kenan a mako guda.

Ana sayar da kwalin taliya a kasuwar Giwa jihar Kaduna kan kudi N17500 a makon nan, yayinda aka sayar da kwalin N19500 a makon daya shude.

 DCL Hausa Maimuna Hadi Ibrahim.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp