Barayin daji sun kutsa kai asibiti, sun sace malaman jinya a Kaduna

Barayin daji sun kutsa kai asibiti, sun sace malaman jinya a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan jinya a cibiyar kiwon lafiya matakin farko da ke kauyen Layin Dan Auta da ke gundumar Kuyello a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna.


A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun far wa wata makarantar firamare da ke Kuyello, a wajen garin.


Sai dai kuma da suka kasa samun daliban da za su yi garkuwa da su, an ce sun koma asibitin da ke kusa inda suka yi awon gaba da ma’aikatan jinya da ke bakin aiki.


Wani shugaban al’ummar yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana lamarin a matsayin abin damuwa.


Yace suna isa unguwar suka wuce kai tsaye wata makaranta da ke kusa da su, a zatonsu za su sami dalibai. Sai dai makarantar babu kowa, don haka suka wuce PHC da ke Kuyello suka yi awon gaba da ma’aikatan jinya da ke bakin aiki,


Shi ma wani shugaban matasan Kuyello, Baba Isah ya tabbatar da faruwar lamarin.


Ya bayyana cewa ma’aikatan jinya biyu suna bakin aiki lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari. Har yanzu dai ba a san ko an sace wasu majiyyata ba, saboda yawancin sun bar asibitin.


Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma ta ‘yan sanda.


Kuma an kasa samun wayar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp