Babu wani tsamin danganta tsakanin Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kasshim - Fadar Shugaban kasa


Fadar Shugaban Nijeriya ta sa kafa ta shure rade-radin da ke yawo cewa akwai tsamin danganta tsakanin Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kasshim Shettima.

A cikin wata sanarwa daga mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai a ofishin Mataimakin Shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ta ce Sanata Kasshim Shettima na samun dukkanin goyon baya da hadin kan da ake bukata wajen tafiyar da gwamnati daga bangaren Shugaba Tinubu.

Nkwocha ya musanta cewa akwai sagwangwanin rashin jituwa a tsakanin shugabannin biyu, yana mai cewa Sanata Kasshim Shettima mutum ne mai biyayya kuma ana damawa da shi a dukkanin harkokin tafiyar da mulkin Nijeriya.

A cikin sanarwar bikin cika shekaru 58 a duniya na Sanata Kasshim Shettima, Stanley ya bayyana wadannan rade-radi da cewa ba su da tushe bare makama ya kuma bukaci mutane su yi watsi da su.

Post a Comment

Previous Post Next Post