Babu wanda zai iya kunna wuta a jiha ta-Bala Muhammad ya mayarwa Wike martani
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce babu wanda zai iya kunna wuta a Bauchi "saboda muna da adadin ruwan da za mu iya kashe wutar".
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP a ranar Talata.
Ya ce muna tare babu wanda zai iya saka wuta a Bauchi domin muna da ruwa mai yawa wanda zai kashe wutar, watakila na fadi wani abu da ya bata wa abokina rai amma abinda nakeso ya sani shine aikina shine jagororanci kuma dole in tsaya a kan hakan.
Wannan dai shi ne karon farko da gwamnan ya mayar da martani kan barazanar Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, wanda ya zargi gwamnonin PDP da yin katsalandan a batutuwan da suka shafi mulkin jihar a Ribas.
A wani taro da aka yi a tsakiyar watan Agusta, gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP, sun ayyana Siminalayi Fubara, da suka rabu da Wike, a matsayin shugaba a jihar kuma shine jagoran jam’iyyar PDP a Rivers.
Hakan dai ya harzuka Wike wanda tare da magoya bayansa suka shirya wani taro a jihar domin kara karfafa musu gwiwa a jam'iyyar PDP ta Rivers.
Da yake magana a taron, Wike ya ce, indai muna raye ba wanda zai kwace mana tsarin PDP. Amma ina gaya wa mutane, na ji wasu gwamnonin suna cewa za su karbe tsarin su mayar wa wani, ina tausayin wadannan gwamnonin domin zan kunna wuta a jihohinsu.