Ba ni da asusun ajiya a banki - Sarkin Daura

 Ba ni da asusun ajiya a banki - Sarkin Daura




Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faroqu Umar ya ce ba shi da asusun ajiya ko daya domin shi mutum ne mai tsoron kudi.


Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin da ya tarbi gwamna Dikko Radda a fadarsa ta Daura.



"Ni Sarkin Daura wallahi ba ni da akawun a banki kuma ko nawa na samu kashewa nake domin ina tsoron kudi


Idan yau na samu Naira milyan goma wallahi ba ta kwana 3 ba ni da ita, ina tsoron kudi domin su kudi bala'i ne su ke kai mutum wuta ni kuma Aljanna nake so ba wuta ba" in ji Sarkin na Daura

Post a Comment

Previous Post Next Post