Manya-manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya na tattaunawa kan yiwuwar hadaka gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Abdullahi ya ce, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don ceto Nijeriya a cikin kangin da jam’iyyar APC ta cefa kasar a shekarar 2027.