ASUU ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami'ar Gombe

ASUU ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami'ar Gombe

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta sanar da yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) bisa la’akari da wasu matsalolin walwalar ma'aikata.


Da yake zantawa da manema labarai a ranar Larabar nan, shugaban kungiyar ASUU reshen jihar, Dakta Suleiman Salihu Jauro, ya ce yajin aikin ya zama dole sakamakon rashin kayan koyo da koyarwa a jami’ar.


Ya ce a cikin shekarun da suka gabata, kungiyar ta yi kokarin wasu dabaru tare da warware matsalolin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.


Wasu daga cikin batutuwan sun hada da rashin aiwatar da yarjejeniyar aiki (MoA) na shekarar 2021 tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin jihar, kan karin kudade ga jami’ar da kuma rashin biyan kudaden da aka tara na Academic Allowances (EAA).


Sauran manyan abubuwan da ke cikin shirin MoA na 2021 da gwamnati ta soke shi ne samar da Naira miliyan 50 ga jami’a a duk shekara.


Ya ce kusan shekaru hudu da rattaba hannu kan yarjejeniyar, har yanzu gwamnatin jihar ba ta biya kobo.


Shugaban na ASUU ya koka da cewa rashin biyan kudin EAA sama da shekaru biyar ya sa ma’aikatan ke ci gaba da fuskantar matsaloli wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu duk da rashin yanayin aiki mekyau.


Ya bayyana cewa akwai kuma batun rashin biyan bashin karin girma na shekaru hudu da rashin aiwatar da kashi 35 cikin 100 na albashin ma’aikata da kuma kashi 25 na albashin ma’aikatan ilimi.


Kungiyar ta ce gazawar da gwamnati ta yi wajen mutun ta yarjejeniyar ya sa kungiyar ba ta da wani zabi illa ta shiga yajin aikin da ba a taba gani ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp