Hukumar zaben Nijeriya INEC ta ayyana Mr Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar Edo da aka gudanar a wannan Asabar.
Babban baturen zaben Prof Faruk Adamu Kuta na jami'ar Gwamnatin tarayya da ke Minna ne ya ayyana sakamakon zaben.
Okpebholo ya samu kuri'u 291,667 yayin da ya kayar da abokin karawarsa na PDP Asue Ighodala da ya samu kuri'u 247,274, sai Dan takarar jami'iyyar Labour Party Olumide Akpata, da ya zo na uku da kuri'u 22,763.