Jam'iyyar APC a jihar Kano ta caccaki jagoran Kwankwasiyya, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, kan sukar tsarin da gwamnatin tarayya na rabon kayan abinci a jihar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaban Jam’iyyar, Abdullahi Abbas, ya ce Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen ganin an kawar da yunwa a kasar, amma gwamnatin NNPP a Jihar na kawo cikas ga kokarin.
Abbas ya kuma musanta zargin Kwankwaso na cewa rabon kayan ga yan Jam’iyyar APC ne kawai.
Shugaban jam’iyyar APC ya ci gaba da cewa, duk da gargadin da gwamnatin jihar ta yi na cewa za ta tunkari duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da kayan abinci, amma an gano manajan Darakta na KASCO, Dakta Tukur Dayyabu Minjibir da hannu a sayar da hatsin gwamnatin jihar.