Ana zargin wani jami'in tsaron 'Civil Defence' da kai wa barayin daji alburusai da kwayoyi a jihar Zamfara
DagaAbdullahi Garba Jani -
0
Rundunar tsaron 'Civil Defence' a jihar Zamfara ta sha alwashin cewa za ta hukunta wani jami'inta Maikano Sarkin Tasha da ake zargin da kai wa barayin daji alburusai da kwayoyi a jihar.
Kwamandan hukumar a jihar Sani Mustapha ya shaida wa gidan manema labarai cewa 'yan sanda ne suka damke wanda ake zargin a yankin Damba zuwa Sabon Gida a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa garinsu, Mada ta karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.