Jami'an Kwastam sun sanar da kama tirela shakare da kasusuwan jakkai da aka kiyasta kudinsu na iya kaiwa Naira milyan 150.
Jami'an na Kwastam da ke karkashin shirin sintirin kan iyaka na Joint Boarder Patrol Team sun kuma sanar da kama wasu karin kayayyaki da suka ce an haramta shiga ko fita da su Nijeriya.
Jami'an hadin guiwa na sintirin kan iyaka na JBPT a shiyyar arewa maso Yammacin Nijeriya karkashin jagorancin Compt. na Kwastam Aminu Abubakar sun sanar da cewa sun kama wannan tirela shakare da kasusuwan na jakkai a titin Gusau zuwa Sokoto.
Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce ana amfani da wadannan kasusuwan wajen hada maganin karfin Maza da sauran haramtattun abubuwa.
Babban jami'in da ke Kula da shirin Comptrolan Kwastam Aminu Abubakar a lokacin zantawa da manema labarai a Katsina, ya ce jamiansu sun kama buhuna 67 na takin zamani da aka kama a titin Sokoto zuwa Kebbi da kuma kama katan-katan na taliyar Spaghetti 175 da jarkoki 50 na man girki da katan 90 na maganin feshin kwari da kuma dilolin gwanjo 62.
Haka zalika, jami'an sun kama buhu shakare da tabar Amuru da ake shakawa da dame 120 na tabar wiwi da nan take ta hannanta ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a jihar Katsina.