Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kama shugaban makarantar firamare ta Gaidar Makada da ke karamar hukumar Kumbotso bisa zargin sayar da kadarorin makarantar.
Hakan na a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Kabir Abba Kabir, ya fitar ranar Asabar. Yana mai ce wa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu na sayar da muhimman kadarorin makaranta ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa hukumar na binciken lamarin, kuma ana kokarin kwato kadarorin da aka salwantar.