An hana wasu matasan NYSC shiga sansanin da ake horar da su na jihar Kano


Wasu matasa da za su yi wa kasa hidima na NYSC na can bakin kofar shiga sansanin da ake horar da su na Kusalla da ke karamar hukumar Karaye ta jihar Kano sun gaza shiga ciki.

Wani matashi da ya nemi jaridar Daily Trust ta sakaya sunansa, ya sanar cewa an hana su shiga ne saboda dalilan da ake kyautata zaton cewa sun je sansanin a makare.

Majiyar ta ce mafi yawan wadanda aka hana shiga din sun zo ne daga wurare masu nisa daga kudanci da gabashin Nijeriya da suka samu tangardar ababen hawa a yayin zuwansu Kano din.

Majiyar ta ce sun sha wahalar tafiya a hanya, wasunsu sun kwashe kwanaki 2-3 gashi sai a kurarren lokaci aka tura musu takardar iznin shiga sansanin matasan na NYSC wato "Call Up Letter".

Ya ce sun kusa kai su 100 da aka hana shiga wannan sansani.

Post a Comment

Previous Post Next Post