An fara cacar baki tsakanin hedikwatar jami'iyyar APC da wasu 'yan yankin Arewa ta tsakiya kan batun Ganduje a shugabancin jami'iyyar na kasa


Wasu jiga-jigai a jami'iyyar APC a yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya sun fara nuna yatsa tare da zargin cewa an ba wasu kusoshin jami'iyyar cin hanci domin su ci amanar yankin wajen shugabancin jami'iyyar da ya kamata a basu.

Wannan tataburza dai na zuwa ne ana dab da gudanar da taron kusoshin jami'iyyar na NEC meeting a ranar 12 ga wannan watan na 
Satumba.

Gamayyar kungiyoyin jami'iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya ne suka yi zargin cewa an dauki wasu mutane aikin yi wa yankin zagon-kasa duk don dai a kyale Abdullahi Ganduje ya cigaba da shugabancin jami'iyyar.

A cikin wata sanarwa daga Shugaban gamayyar kungiyoyin Saleh Abdullahi Zazzaga da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce akwai bare-gurbin da suka fito daga yankin da ake so a yi amfani da su domin mara baya ga shugabancin Ganduje.

Saleh Zazzaga ya ce wannan yunkuri nasu ba zai sare musu guiwa ba wajen nemar wa yankinsu kima da mutunci a idon duniya tare da dakile masu kwadayi da son abin duniya, da suke fifita samun duniya fiye da cigaban al'ummar su.

Shugaban kungiyar ya ce bayan murabus da Abdullahi Adamu ya yi daga shugabancin jami'iyyar na kasa, wanda ya fito daga jihar Nasarawa ta yankin, bai kamata a dauke wannan mukamin ba a kai shi wani yanki na daban ba.

A wani labarin ma, kungiyar magoya bayan jami'iyyar APC ta yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta sanar da ba Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule wa'adin mako daya na ya fito ya nemi afuwar 'yan yankin bisa kalamansa da ke nuna goyon bayan Abdullahi Ganduje a shugabancin jami'iyyar na kasa.

Kungiyar ta hannun shugabanta Hon Sale Abdullahi Zazzaga ta ce na daga cikin tarihi marar kyau da Abdullahi Sule zai bari a yankin idan ya cigaba da tafiya da irin wannan ra'ayin da ya ci karo da ra'ayin duk wani dan yankin da ke son a kawo cigaba.

Sanarwar ta ce idan Gwamnan na jihar Nasarawa bai nemi afuwar mutanen yankin ba, ta nuna karara kansa yake so, ba abin da al'umma ke so ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post