Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 20, tare da raba mutane 3,000 da muhallansu a yobe

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 20, tare da raba mutane 3,000 da muhallansu a yobe

Akalla mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a cikin makonni biyun da suka gabata a Gashua, karamar hukumar Bade a jihar Yobe sakamakon rugujewar gidaje bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya.


Shugaban na karamar hukumar, Babagana Ibrahim ya shaidawa wakilin gidan talabijin na Channels cewa, yanzu haka mazauna yankin da dama na samun mafaka a wasu sansanoni uku da aka kebe.


A cewarsa, gwamnati na samar da agaji na gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu kamar kayan abinci, kula da lafiya,ruwan sha mai tsafta, da abinci don kare su daga barkewar wata cuta.


Yace mutanen da suka rasa matsugunansu ya haura kusan 3,000 muna bukatar gwamnatin tarayya da hukumomin bayar da agaji don tallafawa jahohi da kananan hukumomin da ambaliyar ruwa ta shafa wajen samar musu da kayan agaji.


A kwanakin nan ana ruwan sama kuma gidaje da dama suna rugujewa musamman gidajen laka.


Tuni dai aka rufe hanyoyin biyu na gwamnatin tarayya zuwa Gashua a cikin kwanaki goman da suka gabata, lamarin da ya sa ma'aikatan agaji ke shan wuya kafin isar su wajen 'yan gudun hijirar.


Shugaban ya umurci wadanda ke zaune a gidajen laka da su fice domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp