Akwai shawarar da muke shirin bayarwa na kara harajin VAT zuwa 10% a Nijeriya - Kwamiti

Kwamitin shugaban kasa na farfado da tattalin arzikin Nijeriya ya ce akwai wata shawara da suke shirin badawa ga majalisar dokoki ta kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10%.

Shugaban kwamitin Taiwo Oyedele ya sanar da hakan a wata zantawa da shi a gidan talabijin na Channels.

Sai dai shugaban kwamitin ya ce su na nan su na duba yiwuwar jimilce harajin da ake da su waje daya domin sake yin bita a rage musu yawa a kasar.

Oyedele ya ce wannan shawara da suka rubuta za su hannanta ta ga majalisar dokokin Nijeriya domin duba abin da zai yiwu

Post a Comment

Previous Post Next Post