Zanga-zangar rashin Sarkin Gobir, ta sa gwamnatin jihar Sokoto kakaba dokar hana fita


Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kafa dokar hana fita a karamar hukumar Sabon Birni a jihar, bayan da matasa suka tayar da tarzoma kan kashe sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa.

Kakakin rundunar, ASP Ahmed Rufa’i, ya ce ba za a yarda da wani motsi a yankin daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma ba har sai an samu sanarwar da ta sauya hakan.

Ya ce an dauki wannan matakin ne don dawo da doka da oda a yankin.

Daruruwan matasa sun cika wasu manyan hanyoyin yankin tare da kunna wuta a manyan tituna.

 An kuma ce matasan sun banka wa sakatariyar jam’iyyar APC ta karamar hukumar wuta tare da kone wata kotu.

Haka kuma sun balle wani rumbun ajiya na gwamnati na karamar hukumar inda suka lalata takin zamani.

Post a Comment

Previous Post Next Post