Zanga-zangar adawa da sauye-sauyen Tinubu ba abin mamaki ba ne – Ganduje

Zanga-zangar adawa da sauye-sauyen Tinubu ba abin mamaki ba ne – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zanga-zangar adawa da shirin kawo sauyi da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a fadin kasar bai kamata a yi mamaki ba.


Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jam’iyyar APC reshen Amurka a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.


Ya ce, “Ko shakka babu, a matsayinsu na kasashe masu tasowa, hatta a kasashen da ake kira kasashe masu ci gaban tattalin arziki, suna da rudani. Don haka, ba abin mamaki ba ne cewa Nijeriya tana da nata matsalar. Wannan ba shine karo na farko ba da ake zanga-zanga ba.


“Za ku iya tuna cewa a duk lokacin da ake shirin yin gyara dole ne a samu cikas, a sakamakon haka, dole ne mutane su sha wahala ta wata hanya. Amma, a cikin dogon lokaci, komai zai zama tarihi. Muna sane da cewa shugaban mu Bola Ahmed Tinubu ya shigo da niyyar kawo gyara a Nijeriya.


"Don haka,shugaban kasa yana yin duk abin da ya kamata a yi, kuma nan da wani lokaci za mu fita daga cikin wannan yana yi saboda yana aiki tukuru kan tattalin arziki kuma nan ba da jimawa ba za mu ga sakamako mai kyau.”


Ya ba da tabbacin cewa sauki na nan tafe, ya kara da cewa tasirin gyare-gyaren Shugaba Tinubu zai haifar da sakamako mai kyau.

Post a Comment

Previous Post Next Post