Zan bayyana gaskiya idan lokaci ya yi -Mele Kyari
Shugaban kamfanin samar da man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya ce zai bayyana gaskiya game da ayyukan kamfanin a bangaren mai da iskar gas a lokacin da ya dace.
Kyari ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake ba da shaida a gaban kwamitin rikon kwarya na majalisar dattawa da ke binciken zagon kasa a harkar man fetur.
Kwamitin wanda Sanata Opeyemi Bamidele ke jagoranta, yana binciken ayyukan kamfanin mai na NNPL, ne a daidai lokacin da jama'a ke kiraye-kiraye kan yadda ayyukan ma'aikatar ke gudana.
Kyari ya bayyana cewa, NNPCL ba ta da hannu wajen shigo da abubuwan da ba su dace ba, ta himmatu ne wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Ya koka da rahotannin da ake yadawa a kafafen sadarwa, inda ya bayyana cewa ana yi ne don bata sunan NNPCL, da kuma zagon kasa ga tattalin arziki.