Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya ce jam'iyyar PDP za ta dauki shugaba Tinubu aiki ya zama Daraktan yakin neman zaben jam'iyyar PDP a babban zaben kasar na shekarar 2027.
Bala Muhammed ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomin jam’iyyar PDP a jihar a gidan gwamnati da ke Bauchi a ranar Laraba.
“Akwai yunwa a kasa kuma mutane sun fara fushi. Dole ne mu magance matsalolinmu na ci gaba. Babu aikin yi a ko’ina, tsarin ilimin mu ba ya aiki, kuma sabbin manufofin gwamnatin tarayya ba sa aiki.
“Dole ne su fahimci cewa shirin su ne ya haifar da wadannan matsaloli. A madadin ku, ina gaya wa Shugaba (Bola) Tinubu ya canza manufofinsa saboda ba sa aiki ko kadan. Inji Gwamnan na jihar Bauchi