Za a kai gwamnatin Sokoto kara kotun ICC bayan ajalin Sarkin Gobir

Za a kai gwamnatin Sokoto kara kotun ICC bayan ajalin Sarkin Gobir

Kungiyoyin matasa 18 a karkashin kungiyar matasan Afirka masu yaki da aikata ba dai-dai ba sun yi barazanar kai gwamnatin jihar Sokoto gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a tsare.


Shugaban kungiyar, Dr Suleman Shu’aibu Shinkafi, wanda ya bayyana hakan a karshen taron kwanaki 2 da su ka yi, ya ce kungiyoyin sun zargi gwamnatin jihar Sokoto kan sakaci da ta kai ga rasuwar sarkin.


Dokta Shinkafi ya ce kungiyoyin sun baiwa gwamnatin jihar Sokoto wa'adin mako biyu don biyan wasu bukatu ko kuma su kai su kotun ICC.


Bukatun mu su ne; domin korar kwamishinan harkokin tsaro na jihar, da biyan diyya ga iyalan marigayi sarki tare da bayyana ra’ayinsa game da rasuwar Sarkin Gobir.



Ya kara da cewa suna zargin gwamnati da sakaci wajen tafiyar da lamarin. Gwamnati ce ta gayyace shi zuwa Sokoto don wani taro amma ta kasa kare rayuwarsa. Haka kuma an kasa kubutar da shi bayan an yi garkuwa da shi.”


Daily Trust ta rawaito cewa duk kokarin jin ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Bello Sambo Danchadi da babban sakataren yada labarai na gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Bawa don jin ta bakinsu ya ci tura, domin ba su amsa kiran waya ko amsa sakonnin tes da aka aika musu ba.

1 Comments

Previous Post Next Post