Za a bude sashen da zai rika duba lafiyar shugaban kasa da sauran manyan kasa a babban asibitin Nijeriya da ke Abuja

Asibitin kasa da ke Abuja zai bude wani sashe na musamman wanda zai kula da shugabanni, manyan jami’an gwamnati, da sauran shahararrun mutane dake ciki da wajen kasar.

Babban daraktan asibitin, farfesa Mahmud Raji, ya bayyana hakan jiya a Abuja yayin da ya jagoranci wata tawaga zuwa hedkwatar Media Trust Group.

Farfesa Muhammad ya ce za a gina wani gidan zama ko masauki da aka hade da sashen na musamman wanda zai kasance kamar otal mai tauraro biyar ko bakwai domin kula da dukkan nau’ikan manyan baki.

Farfesa Raji ya kuma ce sashen na musamman zai samu dakin gwaje-gwaje na ilimin guba, yana mai cewa a halin yanzu babu wani asibitin gwamnati da ke da irin wannan dakin gwaje-gwajen domin gwajin guba daga abinci ko muhalli a yayin gaggawa ga shugabannin da ke ziyara.

Post a Comment

Previous Post Next Post