'Yan siyasar da suka sha kaye a zaben 2023 ne ke ruruta zanga-zanga a Nijeriya - Zargin matasan APC

Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta zargi wadanda suka fadi zaben 2023 da hannu cikin shirya zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.

Zanga-zangar tsadar rayuwar da aka fara ta ranar 1 ga Agusta ta dakile harkokin tattalin arziki, musamman a Arewa.

Da ya ke karin bayani akan lamarin Shugaban kungiyar matasan jam’iyyar APC mai mulki Comr Olamide Lawal, ya zargi tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, da wasu ma da ya boye sunan su a matsayin wadanda ya zarga da shirya zanga-zangar.

A bangare guda kuma Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Ogun kan Harkokin Matasa, ya nuna rashin jin dadinsa na yadda wasu matasa suka toshe kunnuwansu daga kiran da shugaban kasa ya yi cikin jawabinshi ga kasa baki daya na dakatar da gudanar da zanga zangar.

Post a Comment

Previous Post Next Post