'Yan sanda a Nijeriya sun sanar da kama mutane 30 da ake zargi da daga tutar kasar Russia a yayin da suke gudanar da zanga-zanga a kasar.
Kazalika, rundunar 'yan sandan ta sanar da kama wani mutum mai suna Ahmad Taylor da ake zargi da samar da wannan tuta a Kano da wasu sassan kasar.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya ACP Olumuyiwa Adejobi ya sanar da hakan a hedikwatar rundunar tsaron DSS a wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka kira a Abuja.
Bayanai dai sun ce an samu karuwar masu daga tutar kasar Russia a wasu jihohin Nijeriya irinsu Kano, Kaduna da Katsina a lokacin gudanar da zanga-zangar da ke gudana a kasar.