'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun dakile hare-haren ‘yan bindiga guda biyu tare da kubutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su, yayin da aka halaka wasu masu garkuwa da mutane biyu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin dinnan.
A cewar sa, rundunar ‘yan sandan ta samu kiran gaggawa a ranar Lahadi kan harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Layin Minister, karamar hukumar Malumfashi ta jihar.
Ya ce an yi garkuwa da mutane biyar a yayin harin.
Yace bayan samun rahoton, an yi gaggawar tattara jami’an tare da tura su wurin. Da suka lura da kasancewar ‘yan sandan, ‘yan bindigar sun bude wuta kan jami’an, inda suka mayar da martani da gaggawa.
Ya ce an samu nasarar kubutar da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba, yayin da maharan suka mika wuya ga jami’an, inda suka tsere da raunukan harsasai daban-daban.