'Yan sanda a katsina sun kama masu safarar makamai Uku tare da masu fashi da makami

'Yan sanda a katsina sun kama masu safarar makamai Uku tare da masu fashi da makami


Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan harsasai masu yawa a cikin garin Dutsinma da ke jihar.


A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, wannan na daga cikin gagarumin nasarar rundunar ta samu a yaki da ‘yan bindiga.


Wadanda ake zargin su ne Ahmed Mohammed Kabir, mai shekaru 25, mazaunin Hayin Danmani, jihar Kaduna, Mannir Musa, mai shekaru 25, daga garin Dutsinma, karamar hukumar Dutsinma da Aliyu Iliya, mai shekaru 25, daga kauyen Dankauye ta, karamar hukumar Safana, jihar Katsina.


An kama su ne a ranar 29 ga watan Agustan 2024, da misalin karfe 12:45, yayin da suke kokarin kai harsasai dari bakwai da arba’in (740) ga wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a dajin Yauni, kauyen Ummadau, cikin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, a cewar hukumar. 


ASP Sadiq a yayin da yake zantawa da manema labarai, ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda ake zargin sun karbi harsashin ne daga jihar Nasarawa domin kai wa wani Harisu, wanda ake zargi da hannu wajen shiga ayyukan 'yan bindigar.


A wani labarin kuma, rundunar ta ce a ranar 27 ga watan Agusta, 2024, ta kama wasu mutum uku Abubakar Ibrahim, mai shekaru 35 a kauyen Dunawa, Jamhuriyar Nijar; Abdullahi Nafi’u, m, mai shekaru 35, Madalla quarters, Abuja, da Adam Musa, mai shekaru 36, dan jihar Kano, dangane da laifin fashi da makami a karamar hukumar Baure ta jihar Katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post