'Yan bindiga sun halaka hadimin gwamnan Katsina da matarsa

 'Yan bindiga sun halaka hadimin gwamnan Katsina da matarsa


Wasu ‘yan bindiga sun halaka Salisu Ango, guda daga cikin ma'aikatan gwamna Dikko Radda a kauyen Gyaza dake karamar hukumar Kankia a jihar Katsina da matarsa ta farko, tare da yin awon gaba da matarsa ta biyu.



An bayyana cewa sun halaka mutum daya, tare da raunata wani, sannan sun yi awon gaba da wasu 28 a unguwar Shirgi da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.


An kuma bayyana cewa sun yi awon gaba da wasu dabbobi  da ba a tantance adadinsu ba a kauyen lokacin da suka kai harin harin.


Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wanda aka kashe a matsayin Amadu Suru, wanda aka harbe shi a lokacin da yake kokarin hada dabbobinsa a rumfarsu.



Ya kuma shaida wa Daily Trust cewa maharan sun kai farmaki kauyen ne a daren Lahadi inda suka kai samame wasu gidaje.


Ya ce mata da kananan yara su ne manyan wadanda akai garkuwa da su.


Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Gyaza da misalin karfe 10:00 na dare, inda suka kai farmaki gidan Ango, inda suka harbe shi da matarsa har lahira.

Post a Comment

Previous Post Next Post