Yaki da cin hanci da rashawa na bukatar taron-dangi, in ji Shugaba Tinubu


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga kasashen kungiyar ECOWAS da su amince da kuma aiwatar da daftarin yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa. 

A yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara karo na 6 Na Kungiyar Taron Dangin Yaki Da Cin Hanci da Rashawa Ta Yammacin Afirka (NACIWA) a Abuja, shugaba Tinubu ya jaddada bukatar daukar kwararan matakai da zakewa a yayin yaki da cin hanci da rashawa dake addabar yankin.

Shugaban wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya sanar da bayar da gudummawar ginin ofishin dindindin ga hedikwatar kungiyar ta NACIWA, kana ya bukaci kasashe mambobin kungiyar da su bari a ga yakin a aikace maimakon a takarda, sannan su mai da hankali kan bin ka’idojin shara'a da inganta hadin gwiwar kasa da kasa, tare da baza gaskiya a faifai ga al'umma a yayin yin amfani da albarkatun kasa ko sayo kayayyakin gwamnati.

Shugaba Tinubu ya bayyana illolin cin hanci da rashawa, da cewa wata cuta ce mai karya garkuwar zamantakewa ta hanyar cin amanar jama’a, da gurgunta rarraba albarkatun kasa cikin adalci. 

Don haka a cewarsa , Najeriya ta shirya tsaf don tabbatar da samun nasarar NACIWA a yankunan ECOWAS a babban shirinta na yaki da cin hanci da rashawa .

Taron ya samu halartar manyan baki da dama da suka hada da ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar; Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi; da Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Mista Ola Olukoyede.

Post a Comment

Previous Post Next Post