Yadda mai sana'ar sayar da shayi ya yi ajalin wani matashi bisa zargin satar masa biredi da taliya a Jigawa
Abdulrashibu Ya’u dan shekara 40 mai sana’ar shayi a kauyen Sararai da ke garin Jigawar Tsada a karamar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa ya yi wa Hassan Garba dan shekara 20 dukan tsiya har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ya’u ya zargi Garba da satar masa biredi, da taliyar yara, da kuma fetur.
Da samun rahoton ‘yan sandan sun tura jami'ai wurin da lamarin ya faru, inda suka cafke wanda ake zargin, yayin da aka garzaya da wanda aka halaka zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa,DSP Lawan Shiisu Adam ya ce a lokacin da yake amsa tambayoyi a sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse, Ya’u ya amince da aikata laifin, inda ya bayyana cewa satar da Garba ya yi masa itace ta kara fusata shi, kuma a baya ya sanar da iyayensa, amma ba a dauki mataki ba.
Ya ce a fusace, Ya’u ya daure Garba da igiya, ya yi masa duka da sanda har ya kai ga mutuwarsa.
Makwabta sun ba da rahoton jin kukan Garba na neman agaji amma sun kasa shiga tsakani har sai da jami’an ‘yan sanda suka iso.
Yace bayan kammala bincike, za a gurfanar da Ya’u a gaban kotu domin ya fuskanci shari'a.