Amnesty International ta bukaci gwamnan Kano ya kafa kwamitin gano yadda zanga-zanga ta kazance a jihar


Ƙungiyar kare hakkin bil'Adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya gaggauta samar da kwamitin bincike da zai binciko dalilin da ya sa jami'an tsaro suka yi ajalin masu zanga-zanga mutum 10 a unguwar Kurna da Ƙofar Nassarawa

A wata sanarwa da Babban Daraktan Ƙungiyar a Najeriya Isa Sunusi ya tura wa DCL Hausa, Amnesty ta ce dole ne kuma kwamitin da gwamna Abba zai nada ya binciki irin yadda mu'amalar jami'an tsaro a Kanon ta kasance da masu zanga-zanga da kuma irin hatsaniya da kungiyar ke zargin wasu da aka dauki nauyinsu ne suka haifar, sa'annan ƙungiyar tana buƙatar a samu kwararru da za su yi aikin kuma a yi a bainar jama'a.

Amnesty ta jaddada cewa idan gwamnatin Kano ba ta yi wannan bincike ba, abin zai zamo ƙalubale babba ga tsarin doka, kuma babu abin da zai ƙãra haifar wa illa ƙarin aikata laifuka cikin ganganci wanda dama ke faruwa a Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post